
Fiye da mutane 1,000 suka rasu daga barkewar cutar Ebola a kasar Congo wanda wannan shine karo na biyu da yake da muni a tarihi.
Ministan lafiya Oly Ilunga yace cutar ta lashe rayuka wanda ya fara tun watan Augusta. Cutar ta fara ne tun shekarar 2014 zuwa 2016 a yammacin Afrika a Guinea, Sierra Leone and Liberia wadda ta kashe fiye da mutane 11,000 inda ta yadu har zuwa iyakar Uganda da Rwanda inda a watan Afrilu kungiyar lafiya ta duniya tace kar a sata acikin ciwon gaggawa a duniya.
An sha kai hare hare a guraren da ake bada maganin Ebola inda kungiyoyi masu zaman kansu suka kwashe ma’aikatan suinda suka bar ma’aikatan gwamnati kawai.
An kai kimanin hare-hare 119 tun watan junairu inda 42 kan kayan aikin lafiya, 85 kuma kan ma’aikatan lafiay. Inda aka kashe wasu, wasu kuma suka samu raunuka.
