Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Dr Isa Pantami, Ya ce Duk Wani Yan Nijeriya Da Bashi Da Rajistar Lambar Shaidar Kasa (NIN) Zai Fuskanci Dauri A Gidan Kaso

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Hadiza Alh Garba, Maiduguri

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Dr Isa Pantami, ya ce ‘yan Nijeriya da suka kasa yin rajistar lambar shaidar kasa (NIN) zasu fuskanci barazanar dauri a gidan yari.

Pantami ya yi wannan bayanin ne a wajen taron ministoci karo na shida wanda tawagar ‘yan jarida na fadar shugaban kasa suka shirya a gidan gwamnati da ke Abuja.

Ya bayyana cewa shawarar da aka yanke na daure wadanda ba su da takardar NIN ya yi daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya, yana mai cewa babu wanda zai amfana da ayyukan gwamnati ba tare da lambar ba.

Pantami ya kara jaddada cewa mallakar katin SIM na iya zama na zabi ne, amma NIN ya zama tilas, inda yace bai kamata a gudanar da hada-hada da yawa a kasar ba tare da NIN ba.

A cewar Ministan, akalla ‘yan Nijeriya miliyan 51 ne suka yi rajista na NIN kuma yana da muhimmanci a gudanar da ma’amaloli a kasar da lambar.

Hakazalika, ya sanar da cewa jimillar rajistar katin SIM a duk fadin kasar ta kai miliyan 189.

Ya bayyana cewa daga cikin adadin, miliyan 150 aka kammala rajista yayin da sauran ke da matsalolin rashin rajistar ba daidai ba.

Ministan ya koka kan yadda rajistar SIM din ta kawo kalubale kuma gwamnati ta fara shirin magance su.

Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi watsi da dokar yin rajistar SIM ba saboda dalilan tsaro da suka samo asali daga wata yarjejeniya da aka samu.

Leave a Reply