Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Dalibai 333 Ne Suka Bata A Harin Da Aka Kai Makaranta A Jihar Katsina

masari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari yace yara 333 ne har yanzu baa gani ba bayan harin da aka kai makaantar sakandare ta Kankara dake jihar Katsina ranar Jumaa da daddare.

Yayin da suke karbar tawaga daga gwamnatin tarayya wanda babban mai bada shawara kan shaanin tsaro na kasa Babagana Monguno ya jagoranta yace gwamnan jihar ya bayyana musu cewa dalibai 839 a makarantar.

Masari ya bayyanawa tawagar gwamnatin tarayyar cewa har yanzu suna kan irga yaran da suke dawowa daga cikin dajin inda suka buya.

Haka nan ya bayyana cewa har yanzu ba wata kungiya data kira gwamnatin cewa ita ta kama yaran.

Ministan tsaron kasar Janaral Bashir Magashi ya bukaci jamian soji, yansanda da sauran hukumomin tsaro dasu dauki matakin gaggawa don ceto yaran.

Leave a Reply