Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Chambas Ya Jaddada Bukatar Hadin Kai Don Magance Matsalar Tsaro A Yankin Sahel

CHAMBERS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wakilin sakatare janara na majalisar dinkin duniya a yammacin Afrika da yankin Sahel, Mohammed Ibn Chambas ya jaddada cewa akwai bukatar hadin kai da hadin gwiwa tsakanin manyan masu ruwa da tsaki don kawo karshen matsalar tsaro day a addabi yankin Sahel da Africa gaba daya.

 Ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi  wajen yaye dalibai wanda makarantar yaki ta rundunar sojin Najeriya ta shirya ga wadanda suka kamala kwas na 3 na shekarar 2019 a Abuja.

Chambas, wanda yayi Magana kan bullowar wasu al’adu masu hatsari a yankin Sahel da kuma abinda zai haifar akan tsaron kasa ya bayyana cewa kisan da akayiwa  Mu’ammar Gaddafi na kasar Libya da kuma yawan yadda ake karya doka a kasashen Arewacin Afrika na daya daga cikin manyan dalilai da suka kawo rashin daidaito a yawancin yankunan.

Ya kara da cewa yaduwar makamai ya karu a kasashen yankin sakamakon kwasar ganima da akayi a ma’ajiyar sojoji ta kasar Libya wanda hakan ya kara karfafa karuwar yan adawa, yan aware, yan ta’adda, masu safarar mutane dama sauran kalubalen tsaro.

Shugaban rundunar sojin Najeriya Lieutenant General Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana gagarumar gudunmawa da yake bayar wad a kuma makarantar yakin a matsayin gudummawa mai gwabi a kokarin wanzar da zamana lafiya da tsaro a duniya baki daya.

Related stories

Leave a Reply