Buratai Ya Halarci Taron Tsaro Karo Na 16 A kasar Dubai

Chief-of-Army-Staff-Major-General-T-Y-Buratai
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kimanin mutane 5,475 da ake zargin mayakan Boko Haram ne ake tsare dasu sa’annan an kashe gommai daga cikinsu.

Shugaban dakarun sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai shi ne ya bayyana hakan yayin wani taro karo na sha shidda da aka gudanar a birnin Dubai na yankin hadaddiyar daular larabawa.

Buratai wanda ya samu wakilcin Laftanar Janar Lamidi Adeosun ya ce sun yi nasarar tarwatsa kamfanin ‘kera bama-bamai guda 32 tare da cin ‘karfin ‘yan ta’addan.  

Har ila yau ya ce kiyassin hukumar bada agajin gaggawa ya yi nuni da cewa mayakan Boko Haram sun kasha mutane kimanin dubu 30 zuwa dubu dari tare da sanya mutane sama da miliyan 3 gudun hijira.

Related stories

Leave a Reply