
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da wa’adin Karin lokaci da akayi wa shugaban gidan yari na kasa da shekara daya inda zai fara daga 21 ga watan Yuli na shekarar 2019.
Ja’afaru Ahmed wanda wa’adinsa zai kare karshen wata ranar 21 ga watan Yuli an kara masa lokacin saboda wasu gyare-gyrae da ake a hukumar. Haka nan don cigaban wasu shirye-shirye kan hakkin dan Adam, lafiya, noma, ilimi ga mazauna gidan yarin.
An bayyana hakan a rahoton da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar cikin gida Mohammed Manga ya fitar.

Sakatariyar din-din-din ta ma’aikatar Georgina Ehuriah ta kirayi shugaban na gidan yari da ya gudanar da ayyukan kan yadda aka tsara da kuma habbaka kasar zuwa mataki na gaba da cigaban kasar.
