
Rundunar sojin Najeriya tace ta dawo da zaman lafiya a garin Gudumbali dake karamar hukumar Guzamala dake jihar Borno na yankin arewa maso gabashin Najeriya bayan da mayakan Boko Haram suka kai hari a ranar juma’a da ta gabata.
Mai Magana da yawun sojin Najeriya Brig.-Gen. Texas Chukwu, shi ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu inda yace, jami’an soji shiya na 82 da kuma hadin gwiwar bataliya na 158 ne sukayi taho mu gama da mayakan Boko Haram a ranar juma’a da ta gabata a arewancin kasar.
Yace musanyar wutan ya faru ne a lokacin da mayakan suka kai hari garin, sun kuma kona gidaje da dama amma babu wanda ya samu rauni.
Hadin gwiwar jami’an tsaron yakawo zaman lafiya a yankin inda Brig.-Gen. Chukwu ya yaba da yunkurin su ya kuma jaddada cewa za’a kara yawan jami’an soji a yankin domin cigaba da tabbatar da zaman lafiya.
Ya kuma kirayi al’ummar yankin da su kasance masu sa ido kan shige da ficen sabbin fuska saboda su hana mayakan Boko Haram buya acikinsu.
