
By: Aisha SD Jamal
Bankin duniya ya nada tsohon karamin ministan lafiya na Najeriya, Prof. Muhammad Ali Pate, a matsayin daraktan lafiya, abinci mai gina jiki da kuma yawan jama’a na duniya.
Hakanan an nada Prof. Muhammad Ali Pate a matsayin daraktan kula da kudade na bankin duniyar wanda zai samar da kudaden dallar amurika masu dimbin yawa da za’a gudanar da ayyukan da zasu taimaka wa mutane kafin shekarar dubu da talatin.

Daraktan kungiyar lafiya ta duniya, Tedros Ghebreyesus, ya tayashi murna inda yace yana fatar ganin ranar da zasu fara aiki tare da Pate.
A watan yuli na shekarar 2013 ne Pate ya bar aiki a matsayin karamin ministan lafiya a najeriya inda ya karbi aikin farfesa a jami’ar Duke dake kasar Amurika.
