
By: Babagana Bukar Wakil, Alkali Muhammed, Maiduguri
Mai shari’a Wakil Alkali Gana na babban kotu mai lamba 11 a Maiduguri ya yankewa Abba Yali da Bashir Muktar da kuma Sadiq Abubakar hukuncin shekaru 7 a gidan yari kan yin fashi karkashin sashen doka na 96 dana dari 2 da 99.
Masu laifin sunyi amfani da keke mai kafa 3 mai lamban rajista MAF183 inda suka yi kokarin kwace wayan wata mai suna Amina Abba Modu wanda ya kai kimanin naira dubu 64.
Mai shari’a ya yankewa Abba Yali da Bashir Muktar na Ngarannam hukuncin watanni ko su biya kudin tara na dubu dari.
Sadiq Abubakar wanda ake kyautata zaton jami’in soja ne wanda aka kora a aiki tare da abokin sa Ibrahim Muhammad an yanke musu hukuncin shekaru 7 ba tare da an daura musu tara.
Mai shari’a yace da wuya a rana ba’a samu wani mai keke a ya aikata laifin kwace waya ko jaka ba.
