Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Babban Hafsan Sojan Najeriya Yayi Kira Da A Samar Da Wasu Na’urorin Zamani Don Yaki Da Yan Tayar Da Kayar Baya

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban hafsan hafsoshin sojan kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya ce akwai bukatar amfani fasahohin zamani don karfafa ayyukan yakin da ake yan ta’adda.

Janar Attahiru ya bayyana hakan ne a wajen bude taron karawa juna sani game da atisayen soja a cibiyar sojojin ta kasa, dake Abuja.

Shugaban ya samu wakilcin shugaban hafsoshin soja da kirkire-kirkire Manjo Janar BM Shafa, inda yace Attahiru ya lura cewa Cibiyar tana rayuwa yadda ake tsammani ta hanyar hada hannu da masu ruwa da tsaki kan lamarin don samun cigaba cikin sauri.

Ya ce Cibiyar tana rayuwa daidai da abin da ake tsammani ta hanyar hada kai da kungiyoyin da suka dace tare da kwarewa a cikin hanyoyin fasahohin.

Shugaban Sojojin ya sanar da cewa an samar da kayan aikin don kammala Cibiyar ta dindindin, yayin da ake shirye-shiryen karin kayan aikin da ake bukata.
Tun farko a jawabinsa na maraba, Mukaddashin Darakta Janar na Cibiyar, Birgediya Janar DI Salihu ya ce bitar horarwar tana da nufin bunkasa karfin sojojin Najeriya don tsara aiki da yanke shawara.

Leave a Reply