
Babban bankin Najeriya wato CBN zai saka Naira biliyan 100 a kokarin farfado da ayyukan samar da kayayyakin sawa a kasa.
Rahoton ya fito daga gwamnan babban bankin Mr Godwin Emefiele bayan da yasa hannu kan yarjejeniya tsakaninsa National Cotton Association of Nigeria wasu kamfanoni a Abuja.
Gwamnan bankin ya bayyana cewa shigo da kayyayakin sawa ba bisa ka’ida ba kadai yana lakume kimanin fiye da dala biliyan 4 a kowace shekara .
