Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Ana Sa Ran Za’a Rantsar Da Mohamed Bazoum Matsayin Shugaban Kasar Nijar A Ranar 2 Ga Watan Afrilun

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kotun tsarin mulki ta Nijar ta tabbatar sakamakon zaben shugaban kasa ranar Lahadi , inda ta tabbatar da cewa Mohamed Bazoum na Jam’iyyar Nijar mai mulki ga Demokradiyya da Socialism (PNDS-TARAYYA) a matsayin sabon shugaba.
A rahoton da aka fitarwa manema labarai a gidan Talabijin na kasar ta Nijar Bazoum ya samu kaso 55.66 na kuri’un da aka kada a yayin taron zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Abokin hamayyarsa, dan takarar jam’iyyar Democratic da Republican Renewal Party, Mahamane Ousmane ya samu kashi 44.34 na kuri’un.
Shugaban Kotun Tsarin Mulki na Jamhuriyar Nijar, Bouba Mahamane, ya ce adadin masu jefa kuri’ar ya kai 4,473,121 daga cikin kimanin miliyan 7.4 da suka yi rajista, wanda ya kasance kashi 62.91 cikin dari.

Ana sa ran za’a rantsar da Mohamed Bazoum a matsayin shugaban kasar ta Nijar a ranar 2 ga Afrilun bana, na tsawon shekaru biyar.
A tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar, dan takarar shugabancin kasar da ya samu sama da kashi 50 cikin 100 na kuri’un ne zai lashe zaben.

Bazoum da Ousmane sun samu kashi 39.3 da kuma kashi 16.98 na kuri’un bi da bi a lokacin zagayen farko na zaben shugaban kasar ta Nijar da aka gudanar a ranar 27 ga Disambar 2020.

Leave a Reply