An Tsayar Da Alhaji Mai Mala Buni A Matsayin Dan Takarar Gwamnan jihar Yobe Karkashin jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Yobe Alhaji Umar Kukuri ya tsayar da Alhaji Mai Mala Buni a matsayin dan takarar Gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APC.

Kukuri ya bayyana hakanne a Damaturu yayin amsa tambayoyi daga yan jaridu inda yace sun sa hankali sosai wajen tantance Mai Mala a matsayin dan takarar gwamna sabanin sauran jam’iyyu da basu tsaida yerjejeniya kan yan takarar gwamnonin suba.

Ya ci gaba da cewa an zabi Mala Buni ne sabo da dacewarsa sannan yin hakan ka iya kawo ci-gaba ga Demokradiya dama kyakkyawar shugabanci ga jama’ar jihar kamar yadda suka bi sawun shugaba Muhammadu Buhari wajen zaben sakataren jam’iyyar APC saboda dacewarsa.

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *