An Samu Labarin Mutuwar Shugaban Kungiyar Boko Haram Mamman Nur

boko-haram-group-writes-european-union-over-conduct-of-french-countries-around-lake-chad
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An samu labarin mutuwar shugaban wani bangare na kungiyar Boko Haram wato Mamman Nur a kasashen yammacin Africa, inda mabiyansa suka juya masa baya tare da hallaka sa.
Jaridar National daily ce ta ruwaito cewa Nur wanda a shekarar 2014 ya raba gari da shugaban kungiyar Abubakar Shekau, bayan yayi mubaya’a ga kungiyar ISIS wanda a yanzu suka daura Abu Mus’ab Al-Barnawy d’a ga Muhammad Yusuf wanda ya assasa kungiyar a matsayin shugaban Boko Haram na yammacin Africa.
Wani majiya ta shaida da cewa sun kashe sa ne bayan tsawon lokaci da sukayi suna samun sabani a dalilin rashin jin dadin yadda yake gudanar da shugabancin sa wanda acewarsu Shekau ya fisa iyawa da kuma zama.
Ya zuwa yanzu dai Rundunar sojin Najeriya bata tabbatar da faruwan lamarin ba.

Related stories

Leave a Reply