
Yansandan Najeriya sun bayyana cewa sun kama daya daga cikin wadanda sukayi garkuwa da shugaban hukumar ilimin firamare na kasar Najeriya Dr. Mohammed Abubakar da yarsa mai suna Yasmin Mohammed.
Anyi garkuwa da Dr Mohammed da yar tasa ranar litinin da rana akan babban titin Kaduna zuwa Abuja inda tuni aka kai su inda za’a binciki lafiyarsu.
Mai Magana da yawun rundunar yansandan Frank Mba, ya tabbatar da hakan a rahoton daya fitar ranar Talata da yamma inda ya kara da cewa an kama mutuum daya daga cikinsu haka nan ana nan ana gudanar da binciken yadda za’a kama ragowar.
Haka nan an samu bindigar AK-47 guda daya daga hannun wanda ake zargin wanda yanzu yana hannun jami’an tsaro.
