
Mazauna birnin Maiduguri na cikin farin ciki bayan samun wutar lantarki a yammacin jiya laraba, bayan watanni biyu da jihar ta dauka babu wutar lantarki.
Gidan rediyo Dandal Kura International ta ruwaito cewa, anyi rashin wutan na tsawon watanni 2 ne sakamakon lalata na’urar wutar a bangaren bada wuta day an ta’adda sukayi a babbar hanyar Maiduguri-Damaturu.
Da wasu mazauna ke zantawa da gidan rediyo Dandal Kura, sun yaba irin jajircewa da kamfani rarraba wutar lantar na TCN tayi, da kuma kamfanin wuta na Yola YEDC sai kuma gwamnatin jihar Borno da sauran masu ruwa da tsaki bisa dawo da wutan.

Wani mazauni, Baba Mai Bukar Ndufu yace hakika ma’aikatan sun cancanta yabo musamman ma na TCN da kuma rundunar soji sai matsan tsaro na sa kai dama kuma kungiyar maharba wanda yace sun bada kariya yayin aikin inda ya kara da cewa harma wasu sunci karo da bomb yayin aikin dawo da wutan.
Wata mai suna Zara Machina, ta yabawa gwamna Babagana Zulum bisa gudumawar san a tabbatar da cewa an samu wuta musamman ma da ake cikin kasa da sati 3 na watar azumin Ramadana.
Sai kuma Alai kusa Kankarama dake anguwar Custom, ya nuna farkar hakan ya kara faruwa ganin cewa jama’a sun wahala yayin rashin wutan a yanayin zafi a ake ciki har ma da fuskanta tashin hankali game da yadda za’a gudanar da azumi ba tare da wutan lantarki ba.
