
By:Babagana Bukar Wakil
Majalisar dinkin duniya ta bayyana ranar 3 ga watan Mayu na kowace shekara a matsayin ranar yan jaridu ta duniya don a dinga wayar da kai kan amfanin barin fadin albarkacin baki da kuma tunawa gwamnatoci da su dinga mutunta dokar a bari kowa ya fadi albarkacin bakinsa kamar yadda yake a dokar kasa.
A wani bincike na International Federation of Journalists IFJ ya bayyana cewa an kashe manema labarai 95 a shekarar 2018 yayin gudanar da ayyukansu.
A shekarar ne aka kashe fitaccen dan jaridar nan Jamal Khashoggi wanda yaja hankalin duniya gaba daya, wanda aka kashe a watan Oktoba da ya gabata bayan yaje ofishin jakadancin Saudyya a kasar Turkiyya.
Haka nan Afghanistan ce kasar da aka fi kashe yan jarida inda aka kashe 16 a shekarar da ta gabata, mutum 9 sun mutu a guri guda a Kabul yayin da aka kai wani harin Bam.
Haka nan da dama ya shafesu sakamakon rikicin Boko Haram da yake faruwa a Arewa maso gabashin Najeriya.
