Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

An kaddamar Da Mota Mai Amfani Da Wutar Lantarki

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An kaddamar da mota mai amfani da wutar lantarki wanda dan asalin jihar Sokoto yayi Jelani Aliyu, inda gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yace hakan zai canza yanayin rayuwa da kuma samar da damammaki gay an Najeriya.

Ya bayyana hakan yayin da ya karbi motocin a fadar gwamnatin jihar.

Motar wanda za’a mika ga jihohin Sokoto, Kebbi da kuma Zamfara wanda aka gabatar a Sokoto, an mika ga gwamna Tambuwal wanda makerin motoci na Amurka na shekarar 2004 kuma darakta janar na Automotive Design and Development Council ta kasa.

Gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakai wajen amfani da kwarewar jihar wajen taimaka tare da canza tattalin arzikin jihar dama gwamnatin tarayya a nan gaba.

Gwamnan ya bayyana wasu kwarewar da albarkatun kasa, noma da sauran su wanda yace idan aka habbaka su zasu taimka wajen inganta tattalin arzikin kasa kuma yace ya kamata gwamnatin tarayya ta maida hankalin ta a wannan bangaren.

Daga karshe gwamnan ya yaba da kokarin darakta janar na Automotive Design and Development Council ta kasa inda yace wannan shine karo na farko da ya tuka mota mai amfani da wutar lantarki.

Kuma ya yabawa gwamnatin tarayya wajen taimaka da tabbatar da kasar nan ba’a bari a baya ba wajen kere keren motoci da sauran su.

Leave a Reply