
Dubban ‘yan hukumar kare hakkin dan adam ne suka gudanar da zanga-zanga kan cigaba da tsare shugaban kungiyar Shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, a kasar Ingila.
Anyi zanga-zangar ne a gaban ofishin jakadancin Najeriya a kasar , bayan da wata babbar kotu a abuja ta bayyana kungiyar a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda ranar Juma’a.
A wata hira da manema labarai sukayi da shugaban hukumar Massoud Shadjareh, ya bayyana cewa El-Zakzaky na bukatar yayi tafiya ya bar Najeriya don ya nemi magani.
Shadjareh ya kara da cewa su kansu ‘yan gwamnatin Najeriya sun kasu kashi biyu wasu naso a saki El-Zakzaky wasu naso a cigaba da rike shi.
