
By:Muhammed Alkali, Maiduguri
Mazauna unguwar Silimri da ke cikin birnin Maiduguri na fuskantar matsalar rashin ruwa sakamakon matsalar wutar lantarki da ta addabi garin na kimanin wata biyu.
Wasu daga cikin mazauna yankin da suka zanta da Dandal Kura Radio International sun ce a koyaushe suna amfani da wutar lantarki wajen dibar ruwa daga rijiyoyin burtsatse amma sakamakon kashe wutar yanzu sun dogara ne da masu sayar da ruwa.
Sun kara da cewa suna siyan ruwa a farashi mai yawa daga masu sayar da ruwan kuma tsadar ruwan ya kasance babban batun a cikin yan kwanakin nan a yankin wanda ya sa mutane da dama suka shiga cikin a babban birnin jihar.

Mazauna garin sun kara yin korafin kan cewa cewa lamarin na da matukar tada hankali inda suke kira ga Gwamnatin Jihar da ta magance matsalar cikin gaggawa.
Hakanan lamarin ya addabi unguwanni da dama a cikin birnin na Maiduguri.
