
Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed tare da mataimakin sa sanata Baba Tela, dama uwargidan sa Hajiya Aisha Bala Mohammed hade da sauran jami’an gwamnati sun karbi allurar riga kafin annobar COVID-19.
Dayake jawabi jim kadan bayan karban allurar, gwamna Bala Mohammed yace allurar riga kafin zai taimaka wajen magance cutar kuma ya nuna gamsuwar sa game da yadda manyan malamai da pastoci suka halarci kaddamar war, inda ya bukace su dayin fadakarwa ga mabiyan su game bukatar yin rigan kafin.
Gwamna Bala Mohammed ya kuma godewa hukumar lafiya na duniya WHO, da sauran masu ruwa da tsaki bisa bada rigan kafin da sukayi a Najeriya dama kungiyoyin cikin gida har dana kasashen waje inda ya nemi hadin kai da goyon bayan su wajen magance cututtuka masu yaduwa a kasa.
Ya kuma bayyana alakar gwamnatin jihar da kungiyar UNICEF a Bauchi inda yace kungiyar ta gyara bangare da daman a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin karta kwana na yaki da cutar COVID-19 a jihar sanata Baba Tela yace za’a rarraba riga kafin a dukkan kananan hukumomi 20 na jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Bauchi Dr Aliyu Maigoro yace tuni an bada horaswa ga ma’aikatan kiwon lafiya kan yadda yakamata su gudanar da aiki.
