Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mai bada shawara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin tsaron kasa Babagana Monguno ya karyata zancen da yace kudaden da shugaba Buhari ya ware dan siyan makamai sun bata.

A hirar sa da manema labarai yace sabbin hafsoshin tsaro basu ga makaman da ya kamata a siya da kudaden bane, kuma yace ba’a fahimci zancen sa bane.

Yace shugaba Buhari ya bada isassun kudaden dan siyan makamai, sai dai har yanzu ba’a kawo su bane amma ba cewa yayi an rasa sub a karkashin shugabancin tsoffin hafsoshi.

Leave a Reply