Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa hafsoshin tsaro zasu tsananta ayyukan su kan yan ta’adda, yace duk wanda aka kama dauke da bindigar AK 47 ba bisa ka’ida ba za’a harbe shi.

Shugaba Buhari ya bayyana haka a taron da suka gudanar tare da majalisar sarakunan gargajiya ta kasa a fadar shugaban kasa dake Abuja wanda sarkin musulmi Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 ya jagoranta tare da Ooni na Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.

Sanarwar ya fito ne ta hannun mai bada shawara na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Femi Adesina.

Wadanda suka halarci taron sun hada da mai bada shawara kan harkokin tsaro ta kasa manjo janar Babagana Monguno mai ritaya, sufeta janar na yan sanda Muhammad Adamu, darakta janar na hukumar tsaron farin kaya Yusuf Bichi da kuma darakta janar na hukumar ayyukan sirri ta kasa Amb Ahmed Rufai Abubakar.

Shugaba Buhari ya bayyana irin kokarin gwamnati wajen inganta tsaro a kasa, ya kara dacewa an samu nasarori a gwamnatin sa a yankunan arewa maso gabas da kuma kudu maso kudancin kasar Najeriya.
Ya kuma bayyana rashin jin dadin sa kan harin da aka kai wajen aikin yan sanda tare da kashe jami’an tsaro da yan ta’adda sukayi, kuma yayi kira ga sarakunan gargajiya da suyi amfani da damar su wajen gina yankunan su da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Sarakunan gargajiya wadanda suka halarci taron sun hada da sarkin musulmai, Ooni na Ife, Obi na Onitsha, Igwe Nnaemeka Achebe, Etsu na Nupe, Alh. (Dr.) Yahaya Abubakar, sarki Jaja na Opobo, Dr.

Dandeson Douglas Jaja, sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Suleiman Adamu, sarkin Gwandu, Alhaji Muhammad Iliyasu da kuma Alawe na Ilawe-Ekiti, Oba Adebanji Ajibade Alabi.

Leave a Reply