Najeriya Zata Iya Ciyar Da Kanta – Nanono

Nanono
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan noma da raya karkara Mohammed Nanono ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata bunkasa ayyukan manoma nan bada dadewa bad a fiye da naira biliyan 600.

Nanono ya bayyana hakan a rahoton da daraktan yada labarai na ma’aikatar Theodore Ogaziech yasa hannu yayin day a kai ziyara kamafanin Dangote na sarrafa taki a jihar Lagos.

Acewarsa ya kai ziyarar ne saboda tarurrukan da sukayi da wasu kamfanonin takin zamanin a jihar ta Lagos don duba kamfanoni masu zaman kansu musamman saboda annobar COVID-19 wanda ya shafi samar da abinci, da hasashen za’a samu karancin abinci a shekarar 2021 that would also wanda zai rage matsalar tsadar abinci da ake fama dashi a yanzu a kasar.

Rahoton yace Nanono ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yake saka naira biliyan 600 kan fannin noma inda zata duba kananan manoma da tabbatarwa an samu abinci mai dorewa.

Haka nan Nanono yace kudin za’a rabawa manoma a fadin kasar wanda za’a fara da manoma miliyan 2.4.
San nan yace don kar mutane su shagala su kashe kudaden gwamnatin zata bada taimakon ne ta hanyar raba kayan noma.

Ministan ya kara da cewa rufe filayen jiragen sama da iyakokin kasar sakamakon annobar COVID-19 ya numa cewa Najeriya zata iya cigaba da ciyar da kanta.

Haka nan ya nuna farin cikinsa na yadda kamfanin dangote ya shirya hanyoyin da zai habbaka harkokinnoma, samar da abinci, takin zamani da habbaka tattalin arzikin kasar a shekarar 2020.

Related stories

Leave a Reply