ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno tace ta dauki matakan kare matasan jihar daga rashin nutsuwa ta hanyar samar musu ayyukan yi.

Gwamnan jihar farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana hakan a Biu yayin da yake shirin barin garin bayan ziyarar da yakai karamar hukumar zuwa Maiduguri.

Gwamanan yace a shirye shiryensa na samarwa matasa aikin za’a fara hoarar da matasan kan sana’oi da and ayyukan yi a karshen shirin inda gwamnati zata samar musu ayyukan dogaro da kai cikin al’umma.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin zata hada kai da jami’ar sojojin dake Biu don shirya hanyoyin zaman lafiya da za’a shirya shirye-shirye na gina zaman lafiya, sake gine-gine da cigaban al’ummar yankunan da rikicin ta’addanci ya shafa.

San nan yayi kira ga masu ruwa da tsaki na The Biu, masu ruwa da tsakin, mambobin sufuri, yan kasuwa da matasan Biu dasu hada kansu don cigaban yankin.

Haka nan ya yi kira ga jami’an sintiri, yan kungiyar CJTF da mafarauta da cewa gwamnati zata taimaka musu da kuma tabbatarwa a n basu albashi akan lokaci.

Related stories

Leave a Reply