
Rundunar sojojin Najeria sun kirayi jama’a da suyi watsi da rahoton da ISWAP suke yadawa kan cewa sun kama jami’ansu da makamai a yankin tafkin Chadi.
Rahoton ya fito daga Maiduguri dake jihar Borno State a ta bakin mai Magana da yawun rundunar hadin gwiwa kanal Timothy Antigha, inda yace faifan bidiyon na karya ne.
Ya kara da cewa suna da lissafin duk hare-haren da ISWAP suka taba kai musu kamar a Metele da Baga tsakanin watan Disamba da watan Junairu.
Wata cibiya ta kalubalanci kafafen yada labaran kasashen waje da taimakawa wajen kara ingiza matsalar tsaro a najeriya.
Haka nan wani rahoto ya gano cewa akwai kafafen watsa labaran kasashen waje 25 a Arewa maso gabas kadai wanda yawanci daga kasar Faransa ne da kuma kasashen dake da harshen faransanci.
