
By Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri
Yaune aka gudanar da bikin sallah karama a duniya baki daya ciki harda Arewa maso gabashin najeriya da yasha rikicin ta’addancin Boko Haram.
Duk da hare-haren da ake fama dasu a birnin Maiduguri baban birnin jihar Borno mutane da dama sun halarci sallar idin.
Limamin filin idi na Asar dake unguwar New GRA Maiduguri, Imam Rawana ya bayyana a hudubarsa cewa ya kamata a dinga samu Musulmai da kyawawan halaye.
San nan yayi addu’ar zaman lafiya ga mutanen Borno, Yobe, Adamawa da Zamfara.
