Sojojin Najeriya Sun Nesanta Kansu Da Takardar Da Take Yawo kan Hambare Gwamnatin Buhari

Rudunar sojojin Najeriya ta tsame kanta daga wata takarda da take zagayawa cikin al’umma cewa wata kungiya mai suna Nigerian Continuity and Progress na kiransu dasu bada taimako wajen hambare gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari akan Mulki.

Rahoton ya fito daga mataimakin daraktan yada labarai na rundunar daga rundunar sojin ruwa Kaftin Muhammed Ahmed Wabi inda yace hakan bai dace da demokaradiyya ba kuma sunyi alla wadai da wanda ya rubuta takardar.

Wabi ya kirayi jama’a da suyi watsi da takardar da NCP suke rabawa su basa goyon bayan a kawowa demokaradiyya cikas.

Ya kara da cewa rundunar su na nan nabi dokoki kamar yadda yake a kundin tsarin kasa na bin shugaba Muhammadu Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *