Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Yansandan Najeriya Sun Kama Masu Garkuwa 6 Da ake Zargi A Jihar Kaduna

police-logo1
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Muhammed Nur Ali

Yansanda a najeriya sun kama masu garkuwa da mutane da ake zargi guda shida a kaduna dake Arewa maso yammacin najeriya.

Mai Magana da yawun rundunar DCP Frank Mba ne ya bayyana a rahoton da ya fitar inda yace an kama su ne ranar 11 ga watan Mayu wanda operation puff adder suka kama.

Wadanda ake zargin sune Ayuba Lawal, Saidu Bello, Abdullahi Bello, Adamu Lawal da Umar Sani duk yan asalin karamar hukumar Dan Musa dake jihar Katsina.

Sai kuma Muhammed Sani, Jibrin Shehu, Usman Sani, Musa Garba wadanda aka kama a dajin Akilbu dake Chikwale a karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Ya kara da cewa an samu bindigar Ak47 guda 2, rifles, magazines guda 4 da harsashai 54, bindiga kirar hannu guda 5 da kuma shanu da suka sato guda 200 daga hannun yan bindigar.

Haka nan sun bayyana wasu muhimman al’amura ga jami’an yansanda kan yadda suke garkuwa da mutane a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Mba ya kara dacewa shugaban hukumar Mohammed Adamu ya tabbatar cewa da hadin kan jama’a za’a kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar.

Related stories

Leave a Reply