 Shugaban Muhammadu Buhari Ya Sanya Hannu Kan Dokokin Yaki Da Cutar COVID 19.

Buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin gaggauta baiwa cibiyar yaki da bazuwar cututtuka ta kasa naira miliyan dubu goma da tabukata domin samar da ingantattun kayakin aiki a dakunan ta na gwaje gwajen jirgin ruwa.
Babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafofi yada labarai Mal. Garba Shehu shi ya bayyana haka a cikin sanarwa da ya bayar a Abuja.
Mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana cewa bada kudaden zai taimaka wa hukumar wajen magance kalubalen da take fuskanta wajen yaki da cutar coronavirus a kasar nan.
Yace shugaban kasar ya kuma bayar da umurnin kwaso wasu manyan ma’aikatan cibiyar guda 3 wadanda suka makale a Brazzaville babban birnin jamhuriyar Congoinda suka halarci shirin bada horo wanda hukumar lafiya ta duniya ta shirya.
Yace daukan wadan nan matakai kari ne a kan sanarwar da hukumar yaki da cutar ta fadar shugaban kasa ta bayar da suka hada da rufe kan iyakoki na tudu da hana zirga zirgan jama’a na tsawon mako hudu da mayar da dukkan sansanonin alhazai cibiyoyin killace wadanda suke dauke da cutar ta COVID 19.
Sauran matakan sun hada da umurtan dukkan ma’aikatan gwamnati da ayyukan su bana musamman bane gudanar da ayyukan su daga gida.

Leave a Reply