 Rundunar sojan saman Najeriya ta kashe ‘Yan tayar da kayar baya a dajin Sambisa.

army-logo
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamitin kula da harkokin rungunar sojan sama na Majalisar wakilai ta Tarayya ya yabawa rundunar Sojan saman ta Najeriya saboda lalata wuraren ‘Yan ta’adda da kayayyakinsu a Gujeri dake jihar Borno.

Shugaban kwamitin, Dr. Muhammad Koko dan Jam’iyar APC daga jihar Kebbi shi ya yi wannan yabon cikin sanarwar da ya bayar a Abuja.

Dr. Koko ya yabawa rununar bisa harin da ta kaiwa ‘Yan ta’adda sannan yabaiwa rundunar tabbacin ci gaba da samun goyonbayan a yakin da take yi da ta’addanci.

Yace Babban Hafsan rundunar, Air Mashall Sadiq Abubakar ya tabbatarwa da kasar nan cewa rundunar zata iya sauke nauyin dake kanta na kare kasar nan.

Ya kuma baiwa ‘Yan Najeriya tabbacin cewa kwamitin wanda yake karkashin  kulawa Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila zai tafiyar da ayyukansa da azamar da ake bukata.

Ya kuma yabawa Shugaba Muhammadu Buhari saboda goyon bayan da yake baiwa rundunar ya kuma bukaci al’ummar arewa maso gabas da su ci gaba da baiwa rundunar rahotonni da suka wajaba da zasu taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu. Tunda farko sai da Rundunar sojan saman ta bayar da sanarwa dake cewa harin da ta kai a karkasin shirin Operation lafiya dole ta lalala kayayyakin ‘Yan kungiyar Boko Haram a Gujeri dake dajin Sambisa dake jihar Borno.

Leave a Reply