 Hukumar aikin hajji ta kasa ta mayar wa da alhazai kudade na aiyukan da ba a yi musu ba.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar kula da aiyukan hajji ta kasa ta mayar wa daukacin yan najeriya da sukayi aikin hajji a shekara ta 2019 naira miliyan dari 4 da 65 da dubu 79 da kuma naira 9

A domin haka ta umurci hukumomin kula da jin dadin alhazai na jihohi da su tabbatar sun mayar wa alhazan su kudaden nasu kamar yadda yake kunshe a ka’idojin hukumar kula da hada-hadan kudade ta najeriya.

Hukumar aikin hajji ta kasa tace duk kudaden da jihohi ba su biya alhazan nasu ba kafin karshen shekarar kudi ta 2019 su mayar mata da su

Hukumar kula da aikin hajjin tace an mikawa hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kebbi na ta kason kudaden da zata mayar.

Related stories

Leave a Reply