 Gwamnatin tarayya ta biya kudaden alawus ga masu shirin N power ke bi

Ministar al’amuran aiyukan jin kai da kuma kyautata rayuwar al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouk tace an biya wadanda aka baiwa aiki na shirin nan na N power kudaden alawus da suke bina watannin oktoba da nuwamba.

Bayanin hakan kuwa yana kunshe ne cikin sanarwar da mai taimakawa ministar kan kafofin yada labarai Halima Oyelade ta turowa gidan radio DDK.

Idan za a iya tunawa dai a ranar 2 ga watan disamba na shekarar 2019 ne ministar ta dauki alkawarin biyan alawus din da suke bi kafin ranar 20 ga watan disamba a yayin  wani taron manema labarai inda tace ana shirye-shiryen biyan na su tare da mika shirin karkashin ma’aikatar ta kamar yadda fadar shugaban kasa ta bada umurni.

Tace shirin na N Power yana da ma’aikata na sa kai dubu dari 5 wadanda aka tura su aikin koyarwa da aikin lafiya da kuma malaman gona kuma an tura su wurare daban daban a kasar nan domin bada tasu gudumawar ga kasar najeriya sannan ana biyan kowannen su naira dubu 30 a wata.

Tace a karkashin shirye shiryen guda 4 ana da ma’aikata miliyan 13 sannan kuma an kiyasta cewa akwai mutane miliyan 44 da zasu ci moriyar shirye shiryen a kasar nan.

Ministar ta bada tabbacin cewa biyan kudaden alawus din da akayi ya nuna kudirin da ake da shi na tabbatar da dorewar shirin tare da cimma burin da aka sanya a gaba na kyautata rayuwar yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *