Gwamna Zulum ya Raba Kayan Abinci Da Tsabar Kudi Ga ‘Yan Gudun Hijira Dubu 19.

BORNO STATE GOVERNOR

BORNO STATE GOVERNOR

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya rabawa ‘Yan gudun hijira dubu 19 da dari daya ton 191 na kayan abinci da kuma tsabar kudi wadanda ‘Ya boko Haram suka tarwatsa a jihar Borno.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne lokacin da yake raba kayayykin a garin Gajiram shalkwatar karamar Hukumar Nganzai.

Kayayyakin da aka rabawa mata dubu 7 da dari 8 sun hada da Zannuwa da kudi Naira dubu biyar ko waccensu da Buhuna dubu 38 da 200 na shinkafa da masara da kuma man girki Galon dubu goma sha tara.

A jawabin da yiwa jama’a a karamar Hukumar ta Nganzai, Gwamna Zulum yace za’a sama musu tsaro domin manoma su koma sana’arsu ta ayyukan noma da kuma kiwo.

Yace hakan zai rage musu dogaro  akan agajin abinci da sauran kayayyaki  na jin kai da ake basu.

Gwamnan ya kara da cewa za’a gina karin gidaje ga ‘Yan gudun hijirar da suka koma daga Maiduguri da kuma Monguno.

Ya kuma yi kashedi da cewa  duk wani Ma’aikaci ko ma’aikaciya da su zauna a kananan hukumomin da suke aiki  ba, za’a sallame su daga aiki.

Ya kuma bayyana damuwa kan cewa duk da kyautatuwar yanayin tsaro da aka samu a yankunan kananan Hukumomi. Har yanzu wasu ma’aikatan kananan Hukumomin suna zaune ne a Maiduguri babban birnin jihar.

Wakilin mu ya rawaito mana cewa garin Gajiram mai nisa kilomita saba’in da biyar daga Maiduguri ta bangaren arewa an sha kai masa hare-hare wadanda suka yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Leave a Reply