Gwamna Babagana Zulum ya bude wasu Karin ayyukaa garin biu.

BORNO STATE GOVERNOR

BORNO STATE GOVERNOR

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya bude wasu ayyuka uku a yankin Karamar Hukumar Biu.

Ayyukan ukun da Gwamnn ya bude, shi ya kawo adadin ayyuka goma da Gwamnan ya bude a  bangaren ilimi da lafiya da samar da ruwan sha a yankin Borno ta kudu.

Gwamnan yace wadannan ayyuka da ya bude an yi sune a yankunan kanann Hukumomin Gwoza da Hawul da kuma Biu da nufin kyautata jin dadin rayuwar jama’ar yankunan.

A yayin da yake bude wata babbar makarantar Firamre a Biu, Gwamnan yace ‘Yan Boko Haram sun lalala makaratun Firamare da na sikandire masu yawa a jihar.

Yace babbar makarantar Firamare ta Firamare ta Biu tana da jerin gine-gine uku dake dauke da ajujwa takwas da ofishin malamai da na ma’ikata.

 Sauran ayyukan da Gwamnan ya bude  a Biu sun hada da ginin Sakatariyar Karamar Hukumr mai ofisoshi arb’in da kuma Sakatariyar Hukumar ilimin Firamare mai ofisoshi goma sha hudu.

Gwamna Babagana Zulum ya kuma umarci Hukumar kula da gyaran tituna ta jihar Borno da ta kammala aikin shumfuda titi mai tsawon kilomita  daya da rabi dake titin Baba Nakori a cikin watanni biyu. Ya karada cewa Gwamnatin jihar zata dukufa kan kara shumfada wasu tituna masu tsawon kilomita hudu da rabi a cikin garin na Biu. 

Leave a Reply