An kashe Masunta masu yawa a kusa da kan iyakar Cameroon.

boko-haram
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘Yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe a kalla mutane hamsin a yankin Tafkin Chadi dake iyaka da kasar Camerron da Chadi.  

Maharan wadanda suka yi ‘badda kama tamkar ‘Yan kasuwa inda suka kaiwa mutanen hari a ranar asirin da biyu ga watan Disamba, koda yake dai labarin kai harin wanda ya faru a cikin ‘kungurmin lungu si yanzu yake fitowa.

Kungiyar Boko Haram wacce aka kafa  a Najeriya a cikin shekarata 2009, ta fadada ayyukanta zuwa kasashen Chadi da Cameroon da kuma Niger dake makwaftaka da Najeriya.  

Magajin garin Darak, Mr. Ramat dake yankin arewa mai nisa na kasar Camroon ya fadawa gidan Radiyo na Dandal Kura ta wayar Talho cewa ashirin daga cikin wadanda aka kashe ‘Yan kasar Cameroon ne sannan mutane masu yawa da ba a san inda suke ba.

 An yi Imani da cewa wadanda aka kashen hadakar ‘Yan kasashe daban-daban ne wadanda suke yin Su a tafkin. Tuni dai mazauna yankin suka hada wata kungiya da suka tura yankin da aka kai harin inda suka ga gwarwakin mutane suna yawo akan ruwa.  Gwamnan Yankin, Mijinyawa Bakary ya tabbatar da afkuwar kai harin.

Leave a Reply